November 16, 2022

MAS’ALOLIN FIƘIHU BISA FATAWAR SAYYEDUL KA’ID(DZ)

 

 

Salam…

Wajibin mukallafi a aikin alwala abu 2 ne:
Na farko: Wanke fuska da hannaye.
Na biyu: Shafan Kai da ƙafafu.
Kowanne daga waɗannan ababen (wanke fuska da hannu, shafan kai da ƙafa). Yana da haddin da ya zama dole a kula:

Dangane da fuska:
Muna da tsayin fuska haka faɗi. Tsayin fuska shi ne daga farkon mafitar gashin kai zuwa (ƙarshen) haɓa, faɗi kuwa, miƙidarin babbar yatsar hannunka da yatsar tsakiya (dolenka wajen faɗin fuskar ka ɗan shiga da sashin sajenka, don samun yaƙinin ka wanke dukkan fuskarka. Ba dole sai ka taɓo kunne ba, Amman dai za ka wanke abun da ya ɗan fi faɗin yatsun 2 don samun tabbacin wanke fuskar duk).

Abun da ya shafi hannu: Wajibi ne wanke hannun dama da hagu daga gwiwar hannu zuwa qarshen yatsun hannayen (shima dai za ka yi kamar fuska. Za ka fara wankowa daga saman gwiwar hannun ne don samun tabbacin wanke dukkan hannu, ba ka bar wani lumb’a ba). Abun da ake so wajen wanke hannun shi ne; ruwa ya isa ga dukkan gaɓar hannun da ake wankewa, da hannu ne zaka isar da ruwan ko wanin hannu. (wato za ka iya tara hannun a ƙasan fanfo ruwa ya dira a hannun ya wadatar). Amman shafawa da hannu me danshi kurum (ba ruwa ka ɗibo ka zuba ba) be wadatarwa.

©Shaikh Mujahid Isa.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “MAS’ALOLIN FIƘIHU BISA FATAWAR SAYYEDUL KA’ID(DZ)”