May 28, 2024

MAS’ALOLIN FIƘIHU (52)

—Darasi Na (52)

 

Tare da Shaikh Mujahid Isa

Salam…

Na’am, muna bayanin abubuwan da suke sabbaba (Sanyawa a yi) Taimama, mun yi bayanin guds 3, ga cigaba.

4_ Faruwar Damuwa Ko Cin Mutunci (Misalin tsananin sanyin da baza a iya shanyewa ba, ko za a hantare ka a wulaƙanta ka kafin ka sami ruwan).

5_ Samuwar cuta idan aka yi amfani da ruwan ko tsanantuwar cutar.

6_ Rashin iya amfani da ruwa sanadin hanin shari’a, Misalin tsarkake Najasa wanda wanin ruwa ba zai iya wakiltar sa ba (Din ƙarin bayani; Watan ruwa ne ɗan kaɗan, se ya zama a tufafinka ko jikinka akwai Najasa, gashi ruwan ba zai isa ka kau da Najasar ba kuma ka yi Alwala, to a nan ba a yarda ka yi Alwala ba, wannan ruwan kauda Najasar kurum za ka yi da shi)

WAƊANSU MUHIMMANTAN HUKUNCE-HUKUNCE:

★ Taimamar da aka yi a makwafin Alwala ko Wankan Janaba, Sakamakon rashin yin Alwala na Sabbaba rashin ƙin yiwuwar salla ko taɓa sunayen Allah ko Ayoyin Alƙur’ani Mai Girma kamar yadda rashin wanka na hana shiga Masallaci… To Taimamar da akayi Sanadin tsukewar lokaci (Wanda nai bayaninta a lamba ta 2 cikin abubuwan da suke janyo Taimama) Idan sanadin rahin isashshen lokaci ne ya sa aka yi Taimama, to a nan babu abun da za ka iya yi da ita sai Salla kurum, bazaka iya taɓa sunan Allah ko Ayoyin Alkur’ani da wannan Taimamar ta ƙarancin lokaci ba.

SHARE:
Mas'alolin Fiqihu 0 Replies to “MAS’ALOLIN FIƘIHU (52)”