August 21, 2023

​Manya Manyan Jami’an Diblomasiyyar Iran da Chaina Sun Zanta Ta Wayar Tarho A Safiyar Yau.

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Chaina sun zanta ta wayar tarho a safiyar yau litinin, inda ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya fara da taya tokwaransa na kasar Chaina Wang Yi kan nadinsa a matsayin kan matsayin ministan harkokin wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto manya-manyan jami’an diblomasiyyar kasashen biyu suna kan ci gaban da ake samu a dangantakar kasashen biyu.

Amir-Abdollahian ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an aiwatar da wasu yarjeniyoyi tsakanin kasashen biyu da kyau sannan ya kara da cewa kasashen biyu sun ci gaba mai yawa a yarjeniyar mai dogon zango tsakanin kasashen na shekaru 25. Ya kuma kara jaddada muhimmancin yarjeniyar ga kasashen biyu.

A na shi bangaren sabon ministan harkokin wajen kasar Chaina Wang Yi yay aba da ziyarar da Anir Abdullahiyan ya kai kasar Saudiya a cikin yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma bayyana fatansa na haduwa da shi a taron Brics a kasar Afirka ta Kudu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Manya Manyan Jami’an Diblomasiyyar Iran da Chaina Sun Zanta Ta Wayar Tarho A Safiyar Yau.”