October 16, 2021

Manoma a Taraba sun yi azumi don neman ruwan sama

Daga Danjuma Makeri


Manoma a Taraba sun fara azumi da kuma gudanar da adduo’i don rokon ruwan sama a gonakin su kasantuwar tsayawar ruwan sama a yankin tun makonni da suka gabata.

Wasu daga yankunan da rashin ruwan ya ta’azzara sun hada da Zing, Yorro, Karim-Lamido da kuma Gossol. Rahotanni sun nuna cewa ruwan sama ya yanke a wadannan yankunan tun wasu makonni da suka gabata kana kuma shukoki har ya zuwa yau basu matakin girma ba.

Ta’azzarar yanayin ya tilasta wa manoma a yankin su fara gudanar da adduo’i na musamman da kuma azumi don neman taimakon ubangiji kan lamarin.

Sarkin yankin Mutumbiyu, Jst. Sani Suleiman ya shaida wa manema labarai cewa manoma na tsananin bukatar ruwan sama a wannan yanayin saboda yawancin shukokin su irin Masara da Shinkafa basu kai matakin girbi ba.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Manoma a Taraba sun yi azumi don neman ruwan sama”