March 24, 2024

mamayar Isra’ila ta yiwa asibitocin Al-Amal da Al-Naser kawanya a Gaza.

A yau lahdi jaridar ahlulbaiti ta Hausa ta nakalto daga tashar larabci ta Al-mayadeen cewar kungiyoyin bada agaji a kasar falasdinu sun fitar da labarin cewar,

A cewar kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, mamayar Isra’ila ta yiwa asibitocin Al-Amal da Al-Naser kawanya a Gaza.

Hukumar ta PRCS ta ba da rahoton an yi ta harbe-harbe da kuma harsasai mai tsanani a kusa da asibitocin biyu.

Hakazalika sojojin mamaya na Isra’ila suna gudanar da aiyukansu a kusa da asibitin Al-Amal.

Lamarin ya jefa kungiyoyin likitoci, marasa lafiya, da ‘yan kasar da ke gudun hijira a asibitoci cikin matukar hadari saboda ba su da motsi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “mamayar Isra’ila ta yiwa asibitocin Al-Amal da Al-Naser kawanya a Gaza.”