Mali, Ta Yi Fatali Da Rahoton MDD, Kan Kisan Fararen Hula

“Babu wani farar-hula daga Moura da ya rasa ransa a yayin farmakin da soji suka kai,” in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Mali, Kanal Abdoulaye Maiga ya karanto a gidan talabijin na kasar.
“Mayakan ‘yan ta’adda ne kawai suka mutu.” Inji shi.
Yayin da take Allah wadai da abin da ta kira “rahoton nuna son kai bisa ga wani labari na kage”, gwamnatin ta bayyana mamakinta kan yadda rahoton binciken da MDD ta yi wajen amfani da tauraron dan adam a Moura wajen tattara bayananta, ba tare da izinin gwamnati ba.
Sanarwar ta kara da cewa hakan tamkar kaddamar da wani binciken leken asiri ne da kai hari kan jami’an tsaron kasar da kuma ” makarkashiya kan harkokin soji”.
Alkaluman da hukumar kare hakkin dan adam ta MDD ta fitar sun bayyana cewa kisan gillan da aka yi a Mali shi ne mafi munin tashin hankali da kasar ta fuskanta tun bayan ta’azzarar hare-haren ta’addanci a sassan kasar a 2012.