May 24, 2023

​Majiyar Isra’ila Ta Bada Sanarwan Budewa Jirgin Leken Asirin Kasar Wuta A Cikin Kasar Siriya

Kafafen yada labaran sun nakalto kakakin sojojin HK yana fadar haka, ya kuma kara da cewa duk da cewa wutan bai sami jirgin ba, amma kuma ya takaita ayyukansa ya koma bazauninsa lafiya.

Kafin haka dai a cikin watan Afrilun da ya gabata ma, sojojin HKI sun bada sanarwan faduwar jirgin saman leken asiri na sojojin kasar wanda kuma ake sarrafashi daga nesa ya fadi a cikin kasar Siriya a lokacinda yake aikin tattara bayanai a cikin kasar. Sai dai sojojin yahudawan sun bayyana cewa sanadiyyar faduwar jirgin lalacewar inginsa ne ba kakkabowar makaman sojojin kasar Siriya ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Majiyar Isra’ila Ta Bada Sanarwan Budewa Jirgin Leken Asirin Kasar Wuta A Cikin Kasar Siriya”