September 16, 2021

Majalisar dokokin Kano ta bukaci a kori Shugaban hukumar tara haraji

Daga Baba Abdulƙadir
Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin Ganduje ta sallami shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Kano KIRS, Abdulrazak Datti Salihi daga aiki.
A zaman Majalisar na ranar Litinin da ta gabata ta bakin shugabanta Engr Hamisu Ibrahim Chidari, ta ce takardar da shugaban hukumar ya aike wa hukumar ƙasa da Safiyo ta Kano ta neman kada su baiwa majalisar bayanai ko wasu takardu ya saɓa da sashe na 128 da na 129 na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa laifin ya kuma saɓa da dokar gudanar da aikin majalisar don haka ta buƙaci a tsige shi cikin kwanaki biyu.
Sai dai ya musanta batun cewa ya hana bada jawabin duk da cewa ya tabbatar wa majalisar cewa shi ne ya rubuta tare da aika takardar.
Bayan da majalisar ta ba shi umarnin tafiya ne kuma ta shiga zaman sirri inda a nan ne mambobinta suka amince da bada shawarar korar tasa.
Haka kuma majalisar ta kafa kwamitin mutane 8 domin ya gudanar da bincike kan dalilan sa na hana a bada bayanai ga majalisar.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Majalisar dokokin Kano ta bukaci a kori Shugaban hukumar tara haraji”