January 28, 2024

Majalisar D D Ta Soki Kasashen Da Suka Dakatar Da Bada Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza

Rahoton musamman na majalalisar dinkin duniya kan alamuran falasdinu ya soki kasashen da suka dakatar da taimakawa hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya dake ayyukan agaji a zirin gaza,saboda zarin wasu daga cikin ma’aikatanta da hannu wajen 7 ga watan Oktoba da dakarun gwagwarmya suka kaddamar a Isra’ila

Kwana daya bayan yake hukumaci kan Isra’ila game da karar da kasar Afrika ta kudu ta shigar na zargin ta da kisan kiyashi kan falasdinawa a Gaza, wasu kasashen suka jingine tallafin da suka bawa hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya ga yan gudun hijra a Gaza UNRWA domin Azabatar da miliyoyin falasdinawa da suke cikin mawuyacin hali.

Kasashen da suka dauki wannan mataki sun kadada Amurka Birtaniya Austeraliya Kanada Finland da kuma kasar Netheland, kana sun soke kwangilar ma’aikata da dama dake aiki da hukumar saboda taimakwa yan gwagwarmaya, suma kasasashen Norwy da Ireland sun sanar da bin sahun takwarorinsu.

 

©VoH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Majalisar D D Ta Soki Kasashen Da Suka Dakatar Da Bada Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza”