Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Tsawaita Wa’adin Daina Karbar Tsohon Kudi.

Majalisar Dattawa ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023.
A ranar 15 ga watan Disamba CBN ya fara fitar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1,000, bayan sanya 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar daina karbar tsofaffin takardun kudin.
Wannan na zuwa ne bayan da kudurin da Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno, ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Laraba.
Ndume ya soki wa’adin da CBN ya sanya tun farko, inda ya ce kawo yanzu mutane ba sa samun sabbin takardun kudin a cikin birane ballantana kuma mutanen karkara.
Ya ce idan CBN bai tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudin ba, hakan na iya jefa miliyoyin mutane cikin wahala