June 2, 2024

Mafi karancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta yi ya samu karbuwa daga kungiyoyi masu zaman kansu. .

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya ce N494,000 mafi karancin albashi na kasa da kungiyoyin kwadago ke nema, wanda adadin ya kai Naira Tiriliyan 9.5 zai kawo tabarbarewar tattalin arzikin kasar tare da kawo cikas ga rayuwar ‘yan Najeriya sama da miliyan 200.

A wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Rabiu Ibrahim, ya ce tayin mafi karancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta yi, wanda ke nufin karin kashi 100 cikin 100 na mafi karancin albashin da ake da shi ya samu karbuwa daga kungiyoyi masu zaman kansu. .

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Mafi karancin albashi na N60,000 da gwamnatin tarayya ta yi ya samu karbuwa daga kungiyoyi masu zaman kansu. .”