September 15, 2023

Mafi Girman Musibar Data Sami Al’ummar Musulmi A Ranar 28 Ga Watan Safar!!!

Sheikh Imran Darussalam 

“Wasu daga Sahabbai suka cewa Manzon Allah (S):
Waɗannan Ansar ne a masallaci mazan su da matan su suke yi maka kuka.
Sai yace: meya sanya su kuka?
Suka ce: “Suna jin tsoron mutuwar ka,
Yace: Ku miƙo mini hannayen ku, ya fita har saida ya zauna akan mimbari, sannan ya godema Allah ya tsarkake shi, yace: “Bayan haka, yāā ku mutane! Shin me kuke inkari game da mutuwar Annabin ku? daa wani ya dawwama kafin ni da nima na dawwama a cikin ku, kusani! haƙiƙa ni mai tafiya gurin Ubangijina ne, haƙiƙa na bar muku abinda idan kuka yi ruƙo dashi ba zaku taɓa ɓata ba, littafin Allah maɗaukakin sarki a tsakanin ku, ku karanta shi safiya da maraice, kada kuyi gasa kada kuyi hassada kada kuyi ƙiyayya (a junan ku), ku zamanto ƴan uwa kamar yadda Allah ya umurce ku, kuma haƙiƙa nabari a cikin ku itrah na Ahlulbaiti na, inayi muku wasici dasu…”

– Alamāāli – Sheikh Almufid – Shafi 46.

SHARE:
Makala 0 Replies to “Mafi Girman Musibar Data Sami Al’ummar Musulmi A Ranar 28 Ga Watan Safar!!!”