September 13, 2023

Madoro Ya Fara ziyarar aiki a Beijin

 

Shugaban kasar Chaina Xi Jinping ya tarbi tokwaransa na kasar Venezuela Nicolas Madoro a safiyar yau a birnin Bejin ya kuma bayyana cewa daga yanzu dangantaka tsakanin Chaina da Venezuela ta musamman ce.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto tashar talabijin ta gwamnatin kasar Chaina na watsa jawabin Xi Jinping kai tsaye, a safiyar yau Laraba. Shugaban ya kara da cewa daga yau dangantaka tsakanin Chaina da Vemezuela ta zama ta musamman, kuma gwamnatin kasar Chaina zaya dauki matakan karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Shugaan ya kuma kara da cewa kasar Chaina kamar yadda ta saba, zata taimakawa kasar Venezuela a kokarin da take yi na tabbatar da yencin kasar da mutuncinta da kuma zaman lafiya a kasar. Har’ila yau zata taimaka wajen kaste hannu kasashen waje daga cikin al-amuran cikin gida na kasar Venezuela.

A nashi bangaren shugaban kasar Venezuela Nicolas Madoro a maida martani ga jawabin shugaban Xi ya ce kasarsa tana alfahari da kasar Chaina a matsayinta na wacce wacce bata mamayar wata kasa, kuma bata kaiwa wata kasa farmiki don kwace arzikin da take da shi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Madoro Ya Fara ziyarar aiki a Beijin”