August 26, 2023

Madagaska : Mutum 12 Sun Mutu Yayin Wani Turmutsitsi A Filin Wasa

Akalla mutane 12 ne suka mutu a ranar Juma’a a Madagaska a wani turmutsitsi da aka yi a kofar shiga wani filin wasa da ke babban birnin kasar, in ji Firaministan babban tsibirin da ke tekun Indiya Christian Ntsay.

Rikicin ya afku ne a gaban daya daga cikin hanyoyin shiga filin wasa na Barea da ke Antananarivo, inda dandazon ‘yan kallo kusan 50,000 suka zo kallon bikin bude gasar wasannin tsibirin tekun Indiya karo na goma sha daya.

Ntsay ya shaidawa manema labarai a gaban asibitin da ke babban birnin Malagasy inda aka kai wadanda suka jikkata, “Alkaluma na wucin gadi ya nuna mutane goma sha biyu ne suka mutu” da kuma wasu 80 da suka jikkata.

A cewar kungiyoyin agaji na Red Cross, adadin zai iya haura.

Shugaba Andry Rajoelina, wanda ya halarci bikin wasanni, ya yi kira da a yi shiru na minti daya.

©voh

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Madagaska : Mutum 12 Sun Mutu Yayin Wani Turmutsitsi A Filin Wasa”