December 17, 2022

ma’aikatar kimiya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayyar Najeriya ta kaddamar da taron karawa juna ilimi na tsawon kwanaki uku

A ranar 15 ga wata ne ma’aikatar kimiya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayyar Najeriya ta kaddamar da taron karawa juna ilimi na tsawon kwanaki uku wanda ya mayar da hankali kan yadda za a samar da hasken wutan lartarki mai karfin Megawatt 30 a kananan hukumomi biyu dake jihar Sokoto a arewa masu yammacin Najeriya.
An dai gudanar da taron ne a Jami`ar Usman Danfodio dake Sokoto, kananan hukumomin Shagari da Bodinga ne za su amfana da wanann shirin.
Wakilin mu dake tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto a kan taron.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “ma’aikatar kimiya da fasaha da kirkire-kirkire ta tarayyar Najeriya ta kaddamar da taron karawa juna ilimi na tsawon kwanaki uku”