January 15, 2023

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa bayan tattaunawa har sau biyar a birnin Bagdaza na kasar Iraki, kasashen Saudia ta Iran sun amince zasu bude kananan ofisoshin jakadanci a biranen Mashad da Jedda.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ministan harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a ziyarar da ya kai kasar Lebanon a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa bude kananan ofososhin jakadancin kasashen biyu a Jedda da Mashad zai bawa Iraniyawa damar zuwa ayyukan ziyara zuwa Umra da Madina a duk lokacinda suka ga dama.

Minisyan ya kammala da cewa bayan haka tattaunawa zata ci gaba tsakanin kasashen biyu dangane da maida huldar jakadanci a tsakaninsu bayan an katse ta a shekara ta 2016 bayan da gwamnatin Saudia ta kashe babban malamin addini Ayayullahi Nimr Bakir Nimr.

Kafin haka dai babban bankin ya sanya 31 ga watan Jenerun da muke ciki a matsayin ranar da za’a dakatar da amfani da tsoffin kudaden.

©Hausa tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bada sanarwan cewa bayan tattaunawa har sau biyar a birnin Bagdaza na kasar Iraki, kasashen Saudia ta Iran sun amince zasu bude kananan ofisoshin jakadanci a biranen Mashad da Jedda.”