January 9, 2023

Luguden Watab Kan ‘Aynul-Asad’ Matakin Farko Ne Na Korar Sojojin Amurka Daga Yankin

Sojojin kasar Iran sun kara jaddada cewa luguden makamai masu linzamin da sojojin kasar suka yi kan sasanin sojojin Amurka dake ‘Ainul Asad’ a kasar Iraki jim kadan bayan kissan Janar Shahis Qasim Sulaimani da abokan tafiyansa a shekara ta 2020 mataki na farko ne a shirin kasar na korar sojojin Amurka daga yankin gabas ta tsakiya.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Janar Muhammad Bakiri ya na fadar haka a wani taro na juyayin shahadar Shahid Sulaimani da abokan tafiyansa.

Bakiri ya kara da cewa gwamnatin kasar Iran da kuma kasashe masu turjiya a yankin suna da hakkin daukar fansa a kan ‘yan ta’addan da suka kashe shaida Kasim Sulaimani da abokan tafiyansa, kuma zasu ci gaba da shirin neman daukar fansa har zuwa lokacin da hakan ya tabbata.

A ranar 3 ga watan Jenerun shekara ta 2020 ne tsohun shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada umurni a kashe babban kwamandan rundunar Qudus ta dakarun juyin kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran a lokacinda yake bako ga gwamnatin kasar Iraki.

Labariin ya kara da cewa gwamnatin kasar Amurka ta tsana Janar Kasim Sulaimani ne saboda gagarumin ruwan da ya taka wajen murkushe kungiyar yan ta’adda ta Daesh wacce ta mamaye yankunan masu yawa a kasashen Iraki da siriya a tsakanin shekara 2014 zuwa 2017.

Amurka a fadin wasu jami’an gwamnatin kasar sun kirkiro kungiyar yan ta’adda wadanda suka hada da Daesh ne don rikita kasashen yankin gabas ta tsakiya saboda HKI ta sarara ta ci karenta ba babbaka a yankin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Luguden Watab Kan ‘Aynul-Asad’ Matakin Farko Ne Na Korar Sojojin Amurka Daga Yankin”