April 22, 2024

Lucky Aiyedatiwa Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Ondo A APC

 

An ayyana Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Ondo.

Shugaban kwamitin zaben kuma gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ne ya sanar da sakamakon karshe na atisayen a hukumance a Akure sakamakon tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 17 cikin 18 na jihar Ondo.

Shugaban kwamitin zaben ya ce gwamna Aiyedatiwa ya samu kuri’u 48,569 inda ya kayar da wasu ‘yan takara 15 da suka fafata a zaben fidda gwani da aka kammala ranar Lahadi bayan da kwamitin zaben ya ayyana zaben fidda gwani a ranar Asabar.

A cewar gwamna Ododo, tsohon mataimakin kakakin majalisar a jihar, Mayowa Akinfolarin, ya zo na biyu da kuri’u 15,343, yayin da Cif Olusola Oke ya samu matsayi na uku da kuri’u 14,865.

Da yake jawabi a gaban jami’an zaben jam’iyyar da suka gabatar da sakamakon zaben kananan hukumomin 17, Gwamna Ododo ya bukaci sauran masu son tsayawa takara da su kasance masu biyayya ga jam’iyyar APC tare da marawa wanda ya yi nasara baya wajen ganin jam’iyyar ta lashe kujerar gwamna a zaben watan Nuwamba na wannan shekara.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Lucky Aiyedatiwa Ya Zama Dan Takarar Gwamnan Jihar Ondo A APC”