September 13, 2023

Libiya : Adadin Mamata Sanadin Ambaliyar Ruwa Ya Zarce 5,000

Adadin mutanen da suka mutu sanadin ambaliyar ruwan a birnin Derna ya karu zuwa 5,300, kamar yadda mahukunta a yankin suka bayyana.

Dubban mutane ne suka bace a birnin Derna sanadin ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da aka yi lakabi da Daniel ta jawo a kasar Libya.

“Akalla mutum 5,300 ne suka mutu a birnin Derna kadai,” kamar yadda Tareq al-Kharaz wani mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a Yankin Gabashin Libya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Ya ce an binne akalla gawawwaki 1,300 bayan daginsu sun gane su.

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Libiya : Adadin Mamata Sanadin Ambaliyar Ruwa Ya Zarce 5,000”