September 13, 2023

Lebanon: Amurka Ta Kakabawa Wasu Mutane Masu Aiki Da Kungiyar HizbullahTakunkuman Tattalin Arziki

Ma’aikatar kudi ta kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutane 7 da kuma wasu kamfanoni takunkuman tattalin arziki saboda taimakawa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakaltp Brian Nelson mataimakin sakataren kudi a ma’aikatar kudade na kasar Amurka yana fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ba zata taba barin duk wani wanda yake barazana ga manofofin kasar Amurka a duniya ba.

Nelson ya kara da cewa wadannan takunkumai sun shafi mutane 7 da wasu kamfanoni a Kudancin nahiyar Amurka da kuma kasar Lebanon.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta yi tayin bawa kungiyar Hizbullahi kudade don ta daina adawa da ita da kuma HKI amma kungiyar ta yi watsi da tayin.

An kafa kungiyar Hizbullah a kasashen Lebanon a shekara ta 1982, kuma a cikin nasarorin da ta samu a cikin shekari fiye da 40 da kafata, akwai korar sojojin HKI daga kasar Lebanon da kuma yakar yan ta’adda wadanda Amurka da kawayenta a duniya suka kafa a kasar Lebanon da kuma Siriya. Tare da samun nasara a kansu. Kuma a halin yanzu ta zama babbar barazana da samuwar HKI a yankin gabas ta tsakiya.

 

©Voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Lebanon: Amurka Ta Kakabawa Wasu Mutane Masu Aiki Da Kungiyar HizbullahTakunkuman Tattalin Arziki”