January 16, 2023

Lauyoyin Tsohon Shugaban Mauritaniya Sun Ce Babu Niyyar Adalci A Shari’arsa

Lauyoyin tsohon shugaban kasar Mauritaniya sun koka kan yadda ake tauye masa hakkoki

Sereh Clidor Lee lauyan kasa da kasa dan kasar Senegal da ke jagorantar tawagar lauyoyin masu kare tsohon shugaban kasar Mauritaniya Muhammad Wuld Abdul-Azizi ya ce: Suna jaddada rashin amincewarsu kan matakin tauye hakkin tsohon shugaban kasar tare da bayyana fargabarsu cewa za a yi wa wanda suke wakilta shari’a ce ta rashin adalci a karshen wannan wata na Janairu, saboda ba a gabatar musu da daukacin fayil din zarge-zargen da ake yi kansa ba, duk da ana sauran kwanaki kadan a fara shari’arsa.

A ganawarsa da manema labarai a birnin Nouakchott fadar mulkin kasar ta Mauritaniya ya kara da cewa: Tsohon shugaban yana fuskantar jerin take hakkoki a dukkanin matakan gudanar da shari’arsa. Clidor Lee ya fayyace cewa: Ana son wulakanta tsohon shugaban ne saboda babu wani abin da ke nuni da cewa shari’ar za ta gudana a kan tubalin adalci.

Muhammad Wuld Abdul-Azizi ya shugabanin kasar Mauritaniya ce daga shekara ta 2008 zuwa 2019 kuma yana da shekaru 66 a duniya, ana tuhumarsa da wasu fitattun mutane kimanin 10 bisa zargin almundahana da halasta kudaden haram da kuma wasu tuhume-tuhume da masu gabatar da kara suka yi imanin cewa ya aikata yayin da yake rike da mukamin shugabancin kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Lauyoyin Tsohon Shugaban Mauritaniya Sun Ce Babu Niyyar Adalci A Shari’arsa”