October 10, 2021

Lai Mohammed – Gwamnatin tarayya na cigaba da nasara kan ‘yan ta’adda

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya na cigaba da yin nasara a kan yan ta’adda a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Minista Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a yayin hirar sa da kamfanin dillancin labarai ta Nijeriya (NAN) a birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana wasu yankuna da ke karkashin ikon yan ta’addan kafin shekarar 2015 da kuma yadda gwamnatin tarayya ta kwace yankunan ta hanyar jajircewar hukumar soji da sauran hukumomin tsaro na kasar.

Ministan ya bayyana nasarorin a matsayin jajircewar gwamnatin tarayya na samar da kayan aiki da abubuwan da hukumomin tsaro ke bukata don aiwatar da aiyukan su.

 

Kamar dai yadda kafafen yada labarai suka ruwaito a watannin da suka gabata yadda gwamnatin tarayyar Nijeriya ta siyo jiragen yaki har guda 10, kana kuma an bayyana cewa zuwa karshen watan Oktobar wannan shekarar zata sake siyo karin wasu jiragen guda biyu duk don aiyukan dakile matsalolin tsaro a kasar.

Ministan ya tabbatar da yadda gwamnatin su ke kokari da kuma yadda take nasara kan yan ta’adda, kamar yadda ya bayyana cewa kafin zuwan gwamnatin su a shekarar 2015 kusan kananan hukumomi 13 ne suka fada halin ha’ula’i sanadin yan ta’addan Boko Haram, ya kuma bayyana cewa bayan zuwan gwamnatin su a 2015 ne suka yi tattaki zuwa Bama, Konduga, Kaure da Maiduguri a watan Satumbar 2015; Jim kadan bayan nasarar lashe zabe.

Ya zuwa yanzu an yi nasarar cimma nasarori da dama kan yan ta’addan, kuma har zuwa yau ana cigaba da kokarin yin hakan.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Lai Mohammed – Gwamnatin tarayya na cigaba da nasara kan ‘yan ta’adda”