February 25, 2023
LABARI CIKIN HOTUNA An ga wasu malaman zabe a kan babur dauke da kayayyakin aikin su na zabe a Bauchi

Rahoton Armstrong Bakam ya bayyana cewa da yanzu haka wasu daga cikin maluman zabe na dauke da kayayyakin aikisu na zabe inda suka doshi rumfunan aikin su na zabe.
Hoton dai an dauke shi ne da safiyar yau a Gadan Maiwa dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.
A cigaba da bibiyar shafin mu domin samun labarai kan zabuka a fadi Najeriya.