October 9, 2023

Labarai Daga Gazza.

Mai magana da yawun kungiyar JIHADUL ISLAMI Dr. Tariq Salmi, ya bayyana cewar israila ta shiga badambadama sakamakon kame dukkanin jami’an da ke bata bayanan sirri kan yan gwagwarmaya a barikinsu da aka kama. Kuma an warware dukkanin naurorinsu na ji ko satar bayanai. Yanzu kawai suna can basu ma san me zasu yi.

Tabbas wannan ya dada nunawa duniya cewar hatta hanyoyin da israila ke samu bayanan sirri na yan gwagwarmaya an dakile shi, sannan wannan ya dana tona asirinsu karara cewar ta zama gidan gizogizo wanda kullum sai karya da yaudara.
Wannan ya nuna rauni da kasawa na jami’an leken asirinsu na farar hula da na soji, duk sun samu rauni sosai.
Ya kara da cewar zasu mika wa Israila jami’anta ne kawai idan aka sako Falastinawan dake karkami a hannunsu.

Shi kuwa babban kwamandar rundunar sojan Iran, Janar Hussain Baqare, ya bayyana cewar wannan shammatar da aka yiwa israila ta hanyoyi daban daban (Hybrid warfare) ya sa yahudawan sun yarda cewar wa’adin zamansu a Falastinu wanda aka dubar musu gaskiya ne, kuma ya dada kara kusantowa kusa. Mun fada a baya cewar duk wani yaki da israiala nan gaba a cikin Israialan za’a yi shi, yanzu kam ai sun tabbatar da abin da muke fada a baya din.

Nasir Abu Sidi Khazeem Muhammad

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Labarai Daga Gazza.”