January 13, 2024

KYAKKYAWAN ALBISHIRI GA MASU ZUNUBI!

Marubuci: Al-Baqir Ibrahim Saminaka

Ina kuke masu zunubi, waɗanda ke ɗauke da dakon laifuka, waɗanda hanske ya dusashe daga fisakunsu, waɗanda nauye-nauyen saɓo ya durƙusar da bayansu, masu cuɗanya kai-komo a tsakanin nau’ukan laifuka, waɗanda littafan ayyukansu suna nan cike fal da jerin gwanon munanan ayyukan (Kamar dai ni ɗin nan)?

 

Ku matso ku ji! Ga nan wata kyakkyawar dama ta taho mana… Dama muka samu ta tuba tare da gyara kusakuranmu na baya, dama ce ta sauya kanmu daga “MU” izuwa “MU”, Sauyawa daga tsohuwar rayuwa zuwa ga sabuwa kyakkyawa… A wannan wata ne Rahamar Allah Ta’ala take sauka/kwarara, wata ne mai girma wanda ake ninninka ladan ayyukan kirki, kuma ake yafewa da goge laifuka. kamar yadda ya zo a ruwayoyi masu yawa.

 

RAJAB; WATAN MAMAKON RAHAMA.

Ya zo daga Annabin Rahama (S): “Haƙiƙa Allah Maɗaukakin Sarki ya naɗa wani Mala’ika a sama ta bakwai ana ce masa «Da’i» (Mai kira/shela), idan watan Rajab ya shigo wannan Mala’ikan yana shela a kowane dare zuwa safiya, yana cewa; “Aljanna ta daɗaɗa ga masu ambaton Allah da masu biyayya ga Allah (Masu ayyukan kirki)”

 

Daga nan sai Allah Ta’ala ya ce: “Ni ne abokin zaman duk wanda ya zauna (Don ibada da ambatona), ni mai bin umarni ne ga wanda ya bi umarnina, mai yin gafara ga duk wanda ya nemi gafarata. Wannan watan watana ne, kuma bayin ma nawa ne, sannan Rahamar ma tawa ce. Don haka duk wanda ya roƙe ni a wannan wata to zan amsa masa, wanda ya tambaye ni zan ba shi, wanda ya nemi shiriyata zan shiryar da shi, kuma na sanya wannan wata a matsayin wata igiya ce da ke tsakanina da bayina, saboda haka duk wanda ya yi ruƙo da shi (Ya ribaci wannan watan) to -haƙiƙa- zai iso gare ni”

[Biharul Anwar: 95/377].

 

Madalla! Maraba lale da wannan wata na Rajab ƙofar tuba, wata mai kwaroro ruwan Rahama, wanda zai tafiyar mana da dauɗarmu, ya wanke mana zukatanmu ya kuma tsakake mana ruhinmu, ya ɗauraye mana hanyarmu ta isa zuwa ga Allah. Haƙiƙa watan Rajab wata gwaggwaɓar kyauta ce daga Allah, mu dage iya iyawa mu ci moriyar ta ta dukkan hanyoyin da za mu iya… Ya Ubangiji ga mu mun sabunta ɗamarar kusanto ka, da kai ne kaɗai muka dogara, ka kama hannayenmu ka ƙarfafi gwiwoyinmu, Bi-Muhammdin Wa Ali Muhammad.🤲🏼

SHARE:
Makala 0 Replies to “KYAKKYAWAN ALBISHIRI GA MASU ZUNUBI!”