January 23, 2023

Kwana takwas ya rage a daina karɓar tsaffin takardun kuɗi na ₦200 da ₦500 da kuma ₦1000,

Yayin da ya rage kwamaki 8 wa’adin da babban bankin Najeriya CBN ya sanya domin daina karɓar tsaffin takardun kuɗi na ₦200 da ₦500 da kuma ₦1000, har yanzu al’umma na cigaba da ƙorafi na rashin wadatar sabbin kuɗaɗen a hannunsu.

A ƙarshen makon da ya gabata ne bankin CBN ya sanar da kafa kwamiti da zai shiga yankunan karkara domin musanyawa al’ummar yankunan tsaffin takardun kuɗi da suke hannunsu zuwa sabbi.

Shin ya zuwa yanzu wane hali ake ciki game da sauyin kuɗin a yankunanku?
Wace hanya kuka shirya bi wajen rabuwa da tsaffin takardun kuɗin da ke hannunku?
Wane ƙalubale kuke fuskanta wajen sauya kuɗaɗen naku?

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kwana takwas ya rage a daina karɓar tsaffin takardun kuɗi na ₦200 da ₦500 da kuma ₦1000,”