October 1, 2023

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC na shirin shiga yajin aikin gama gari

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC na shirin shiga yajin aikin gama gari a fadin Najeriya  wanda kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) ta ce mambobinta za su shiga yajin aikin.

janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi da kuma irin illar da ya yi wa ‘yan Najeriya, ya sa ma’aikatan suka yi barazanar shiga yajin aikin gama gari da za a fara ranar 3 ga watan Oktoba a fadin kasar.

Yan kwadago suna neman gwamnati ta kalli haraji, alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati, da rage kudin gudanar da mulki, da kuma biyan albashi bayan cire tallafin man fetur.

SHARE:
Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC na shirin shiga yajin aikin gama gari”