Kungiyar Tarayyar Afrika Ta Zama Mamba A Kungiyar G20

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin da gwamnatocin kungiyar suka hadu a birnin New Delhi na Indiya.
Dama kafin hakan Firaministan Indiya, wanda kasarsa ke shugabancin kungiyar a wannan karo, Narendra Modi, ya bayyana kyakyawan fatansa na ganin gungun kasashe mambobin kungiyar ya fadada, ta hanyar karbar kungiyar AU a matsayin mamba ta dindindin.
Shugaban kungiyar AU, kana kuma shugaban kasar Comoros, Azali Assoumani, shi ne ya karbi kujerar da aka ware wa tarayyar Afrika a matsayinta na sabauwar mamba a G20.
Kungiyar tarayyar Turai mai kujera guda a kungiyar ta G20, ma ta bayyana fatanta game da wannan matakin, kamar yadda shugaban majalisar kungiyar Charles Michel, ya shaidawa ‘yan jarida a New Delhi.
Dama a watan Disamba, shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana fatan shin a ganin kungiyar tarayyar Afrika ta shiga kungiyar ta G20 a matsayin mamba ta dindindin.
Kawo yanzu dai Afrika ta kudu ce kawai wata kasa mamba a kungiyar ta G20, wacce ta kunshi kasashe 19 mafi karfin tattalin arziki a duniya gami da kungiyar EU, wadanda a tsakanin su kunhsi kashi 2/3 na al’ummar duniya.