January 8, 2023

Kungiyar Kwlalon Kafa Ta Iran Zata Aikawa Shugaban FIFA Wasikar Korafi Na Kiran Taken Farisa Da Tekun Larabawa

 

Shugaban hukumar FIFA ta kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino , wanda ya halicci bikin bude gasar gwallon kafa ta wasu kasashen larabawa a birnin Basra na kasar Iraki, a jawabinsa na bude gasar ya ambaci tekun farisa a matsayin tekun larabawa wanda ya sabawa sunan da ake kiran tekun shekaru aro-aro.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Asabar kungiyar kwallon kafa ta kasar Iran ta bayyana korafinta a fili, ta kuma bayyana cewa zata isar da shi a rubuce ga shugaban hukumar ta FIFA.

Gasar kasashen larabawan na yankin Tekun farisa wanda aka fara tun ranar 6 ga watan Jeneru zai ci gaba har zuwa 19 ga watan, kuma zai hada kasashen larabawa na yankin tekun farisa ne wadanda suka hada da Iraki, UAE, Saudia, Kuwait, Bahrain, Oman, Qatar da kuam Yemen. Iraniyawa a duk duniya sun bayyana korafinsu ga yadda shugaban na FIFA yayi amfani da wannan jabun suna ga tekun na farisa.

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Kungiyar Kwlalon Kafa Ta Iran Zata Aikawa Shugaban FIFA Wasikar Korafi Na Kiran Taken Farisa Da Tekun Larabawa”