May 13, 2023

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC ta sanar cewa kasar Angola ta zarta Najeriya wajen hako danyen mai a wannan wata na Afirilu.

Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC ta sanar cewa kasar Angola ta zarta Najeriya wajen hako danyen mai a wannan wata na Afirilu.
Kungiyar ta tabbatar da hakan ne a cikin mujallar ta da ta saba fitarwa a duk wata. Rahoton ya nuna cewa a wannan wata na Afirilu, Angola ta hako ganga miliyan 1.085 na danyen mai, yayin da Najeriya kuma ta samu hako 999,000 ne kawai.
Wakilin mu dake tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya ci karo da rahoton mujallar, ga shi kuma da karin bayani.

Wannan dai shi ne karo na farko cikin wannan shekara ta 2023 da yawan gangar man da Najeriya ke hakowa ya yi kasa.
Najeriya wadda ta kasance kasar Afrika da ta yi fice wajen samar da mai a duniya ta samu koma bayan kudaden shiga daga cinikin mai a shekarar bara, inda kudin shigar da ta samu a bangarorin da ba su shafi mai ba ya kai kaso 59 yayin da kuma bangaren mai yake da kaso 41.
Kaso 90 na abun da Najeriya ta dogara da shi a jerin kudaden shigar ta yana fitowa ne daga bangaren man fetur, an kayyade farashin gangar mai kan dala 75 a kasafin kudin kasar na 2023.
A farkon wannan watan, rahoton ya nuna cewa, Najeriya ta yi lodin ganga miliyan 20 na danyen mai a jiragen ruwa guda 20 wanda kudin su ya kai dala buliyan 1.7, amma kuma a wancan lokaci masu sayen hajar suka dauke hankalin su daga sayen man na Najeriya.
Kamar yadda kungiyar ta OPEC ta bayyana, a cikin watan Fabrailun wannan shekara, Najeriya ta samar da ganga kusan miliyan 1.3 na mai, amma kuma a watan Maris gangan miliyan 1.2 ta iya samarwa yayin da a wannan watan kuma na Afirilu abin ya sake yin kasa inda ta samar da ganga 999,000 kadai.
A sakamakon wannan rahoto, tashar CRI ta samu jin ta bakin masani kan harkokin hada-hadar mai a Najeriya Alhaji Sani Ya’u Babura, ko me yake jin ya haifar da irin wannan koma baya?
“Abin da yake faruwa gaskiya akwai maganar satar gurbataccen mai a Najeriya, ko da yake ko a baya ana samun wannan matsala amma abun ya fi kazanta a wannan lokaci, da can wasu ne kalilan suke sace man, amma a yanzu mutane da yawa suna shiga harkar, mun sani cewa manya manyan masu satar man kuma su suke hako danyen man su ne suke da na’urorin da suke kidaya adadin man da aka hako, ka ga sai abun da suka gayawa Najeriya an samu daga man da aka haka.”
A 2022 ayyukan barayi danyen mai ya yi kamari a Najeriya, lamarin da ya tilastawa wasu kamfanoni yin asarar sama da kaso 90 da abin da suke samu, a wancan lokaci ne ma kamfanin mai na NNPC ya bayar da kwangilar lura da bututun mai ga wani tsohon jagoran ‘yan ta’adda masu fasa bututun mai wanda akewa lakabi da Tompolo domin dai dakile asarar da kasar ke yi a bangaren danyen mai.

©(Garba Abdullahi bagwai)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC ta sanar cewa kasar Angola ta zarta Najeriya wajen hako danyen mai a wannan wata na Afirilu.”