January 28, 2024

Kungiyar Hizbullah Ta Takai Hari Da Makami Mai Linzami a Hedkwatar Sojin Isra’ila.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun gwagwarmayar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kaddamar da hare-hare da makamai masu linzami hedkwatar soji ta isra’ila dake arewacin yankunan falasdinawa da ta mamaye, kuma ya haddasa mummunar Asara a wajen.

A wata sanarwar da kungiyar ta hizbullah ta fitar ta fadi cewa harin da dakarun ta suka kai da makamin mai linzami samfarin Falaq a barikin soji na zabedin dake filin shaba’a na ta Isra’ila ya samu inda ake su koya jikkata sojoji da dama,

Har ila yau t ace makami mai linzami da aka harba an kawatashi da kamarori dake danar bayanai kan yadda harin ke gudana da kuma irin sakamakon da ya haifar, ko jiya ma dakarun na hizbullah sun kai hari a wuraren soji guda 5 a yankin Al-jalil dake Arewacin gabar yamma da kogin Jodan.

 

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kungiyar Hizbullah Ta Takai Hari Da Makami Mai Linzami a Hedkwatar Sojin Isra’ila.”