June 21, 2023

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jinjina wa ‘Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Na Yankin Jenin

 

A jiya Talata ne dai kungiyar gwagwarmayar ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da a ciki ta jinjinawa ‘yan gwagwarmayar yankin Jenin da su shammaci ‘yan mamaya ta hanyar yi musu kwanton bauna da lalata daya daga cikin motocinsu na yaki.

Kungiyar ta Hizbullah ta kuma yi Allah wadai da harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin wanda na dabbanci ne.

Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta kuma yi wata jinjina ga ‘yan gwagwarmayar Palasdinawa akan harin daukar fansa da su ka yi akan sansanin yahudawa ‘yan share wuri zaunana Aily, da yake a Arewacin Ramallah.

A karshe kungiyar gwagwarmayar ta Lebanon ta yi gaisuwa ga shahidai, tare da rokon Allah madaukakin sakri da ya bayar da lafiya ga wadanda su ka jikkata.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jinjina wa ‘Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Na Yankin Jenin”