January 27, 2024

Kungiyar Hizbullah Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Kan Matsugunan Yahudawan Sahyoniya

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai hari kan wasu wurare biyar na sojojin yahudawan sahyoniya a yankin Al-Jalil da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

An kai harin na Hizbullah da manyan rokoki daga kudancin Lebanon.

A gefe guda kuma, kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayar da rahoton cewa, an yi ta buga kararrawar hadari sau da dama a yankunan arewacin Palastinu da ta mamaye.

Ya kamata a lura da cewa a cikin ‘yan kwanakin nan bayan munanan laifukan gwamnatin sahyoniyawan a yankin Zirin Gaza da kuma kisan gillar da aka yi wa wani adadi mai yawa na Palastinawa a wannan birni, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kai hare-hare kan wuraren soji na wannan gwamnati a arewacin kasar a yankunan da aka mamaye. Lamarin da ya haifar da fargabar yahudawan sahyoniyawan da ke zaune a wadannan yankuna.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kungiyar Hizbullah Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Kan Matsugunan Yahudawan Sahyoniya”