June 8, 2024

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce mafi karancin albashi na Naira dubu sittin ga ma’aikatan jihar a duk fadin kasar ba zai dore ba

 

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce mafi karancin albashi na Naira dubu sittin ga ma’aikatan jihar a duk fadin kasar ba zai dore ba saboda yanayin tattalin arzikin da ake ciki a halin yanzu.

Kungiyar ta amince da cewa, ya kamata a kara sabon mafi karancin albashin ma’aikata tare da jajantawa kungiyoyin kwadagon na neman karin albashi.

A wata sanarwa da mukaddashin daraktarta na yada labarai da hulda da manema labarai Halima Ahmed Yakubu ta fitar, kungiyar ta NGF ta bukaci dukkanin bangarorin da su yi la’akari da cewa tattaunawar mafi karancin albashin ma ya kunshi gyare-gyaren da za a iya samu a dukkanin ‘yan kungiyar ciki har da ‘yan fansho.

Kungiyar ta NGF ta gargadi bangarorin da ke cikin wannan muhimmin tattaunawa da su duba fiye da sanya hannu a kan takarda kawai; Duk wata yarjejeniya da za a rattabawa hannu ya kamata ta kasance mai dorewa kuma ta tabbata.

Ya kara da cewa, Jihohin za su kashe duk kason su na FAAC wajen biyan albashi kawai ba tare da wani abu da ya rage na ci gaba ba sannan kuma su ciyo rancen biyan ma’aikata duk wata.

NGF ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa, musamman ma kungiyoyin kwadago da su yi la’akari da duk wani canji na zamantakewar al’umma tare da kulla yarjejeniya mai dorewa, mai dorewa, da adalci ga dukkan bangarorin al’umma da ke da hakki na mallakar dukiyar al’umma.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce mafi karancin albashi na Naira dubu sittin ga ma’aikatan jihar a duk fadin kasar ba zai dore ba”