October 14, 2021

Kungiyar ASUU ta nemi majalisar tarayya da ta hana ma’aikata tura yaran su karatu a kasashen waje

Daga Saddam Alkali


Rahoton da yake zuwa mana daga garin Abuja wurin tattaunawar kunguyar malaman jami’a (ASUU) da kuma wakilan gwamnatin tarayya shine kungiyar ta ASUU ta nemi majalisar tarayya da ta hana ma’aikata tura yaran su karatu a kasashen waje.

 

Kungiyar malaman jami’a wacce da aka fi sani da ASUU ta nemi ma’aikatan gwamnati da su cire ‘ya’yan su daga makarantun kasashen waje kana kuma su dawo dasu su cigaba da karatu a Nijeriya.

Kana kuma kungiyar ta yi kira ga majalisar tarayya da ta samar da dokar da zata tilasta wa ma’aikata masu ofisoshi a gwamnati da su tura wadanda ke karkashi kulawar su izuwa makarantu na cikin gida Nijeriya. Kungiyar ta bayyana cewa daukan irin wannan matakin zai sanya ma’aikata su fahimci lalacewar bangaren ilimi a jami’o’in kasar.

Shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya mika wannan bukatar a birnin Abuja yayin ganawar da kungiyar tayi da wakilan gwamnatin tarayya wanda Ministan kwadago ya walkilta.

Farfesa Emmanuel ya bayyana hakan ne ga manema labarai kafin shigar kungiyar cikin dakin taron, inda yace suna fatan gwamnati zata maida shi doka kan duk wanda ya karbi mukamin gwamnati to dole ya kai ‘ya’yan sa zuwa jami’ar gwamnati.

Ya bayyana cewa yakamata majalisar tarayya ta kaddamar da wannan dokar, ga duk ma’aikacin da bai shirya aika dan sa zuwa jami’ar gwamnati ba to kada ya fara karbar mukamin gwamnati.

Farfesan kuma ya zargi gwamnatin Nijeriya da taka rawar gani wurin lalacewar harkar ilimi a kasar, inda ya buga misali da kasafin kudin da aka gabatar yan kwanakin da suka gabata, Farfesan ya bayyana cewa babu wani abu da ya canza a kasafin ilimi a kasafin.

Daga karshe ya bayyana cewa kungiyar ta ASUU na fafutuka ne don gyara harkar ilimi a kasar, ya kasance kamar yadda yan kasar ke fita wasu kasashe don karatu itama kasar wasu daga wasu kasashe su shigo ta don karatu ta yadda zasu biya gwamnatin kasa kudade masu yawa.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kungiyar ASUU ta nemi majalisar tarayya da ta hana ma’aikata tura yaran su karatu a kasashen waje”