December 14, 2021

Kundin Sulhun Imam Hasan Da Mu’awiya

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

Kundin yarjejeniyar sulhu da Mu’awiya ya tanaji cewa a yi aiki da Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (s.a.w.a), haka nan ya tanaji cewa Mu’awiya ba shi da daman nada wani a matsayin wanda zai gaje shi. Yarjejeniyar ta karbi alkawarin Mu’awiya tsakaninsa da Allah kan cewa ‘yan Shi’ar Ali (a.s.) za su zama cikin aminci a rayukansu, dukiyoyinsu, matansu da ‘ya’yansu.

Hakika al’umma da tarihi sun yiwa Imam Hasan (a.s.) shaida kan cewa ya tsaya kyam a kan sharuddan yarjejeniyarsa da Mu’awiya, alhali daga baya abubuwan da suka faru sun tabbatar da ha’incin Mu’awiya da Umayyawa ga wannan alkawari da karkacewarsu daga Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (s.a.w.a), da yadda suka yi ta kashe bayin Allah daga zababbun al’umma da kwace dukiyoyi da yin fasadi a doron kasa da wasun wadannan na daga laifuffuka da suka bata fuskar tarihi da su.

Hakika Mu’awiya ya fara keta iyakokin yarjejeniyar tun a ranakun farko, inda ya bayyana aniyarsa a fili, yayin da ya tafi Kufa ya hau mumbari a masallacin garin ya fada (a gaban al’umma da tarihi) cewa:

“Wallahi ni ban yake ku don ku yi salla ko azumi ko hajji ko zakka ba, domin ai kuna yin haka; na dai na yake ku ne don in mulke ku, hakika kuma Allah Ya ba ni hakan alhali ku ba ku so. To ku saurara duk wani jini da aka zubar a wannan fitina ya tafi a banza, kuma duk wani alkawari da na dauka yana karkashin kafafuwan nan nawa guda biyu”

 

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Kundin Sulhun Imam Hasan Da Mu’awiya”