November 24, 2022

Kudurin dokar da zai kara wa karatun allo kima

Wasu jihohi sun fara kokarin soke tsarin karatun allo

Kudurin dokar ya nemi a kafa hukumar da za ta dinga kula da tsangayoyi da almajirai da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya musamman a jihohin da ke arewacin kasar.

A yanzu haka kudurin ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan kasar.

Manufar kudurin ita ce samar wa masu karatun allo daraja da hanyar dogaro da kai ta yadda al`umma za ta daina kallonsu a matsayin jahilai saboda ba su yi karatun boko ba.

Hon Shehu Kakale shi ne ya gabatar da kudurin ya kuma shaida wa BBC cewa babban burin  wannan hukumar shi ne ta samar da matsayi da kima da mutunci ga karatun almajirci da tsangaya da makaruntun allo a Najeriya.

‘’Ba  zai yuwu a ce  wanda zai iya karatu da rubutu da Larabci ko ajami ko ya haddace Al’kur’ani sannan a ce mi shi jahili ba. ”

‘’Ko kuma dan Najeriya wanda ke Kudu yana sana’oinsa kan harkar spare part na mota ko kuma  harkar kayan sawa wanda ‘yan Kudu ke yi  duk tarin ilimin shi idan bai iya  Turanci ba ko A B C D a ce mai jahili ba.’’

©Bbc Hausa

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kudurin dokar da zai kara wa karatun allo kima”