June 1, 2023

Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Za Ta Sauya Dabarar Aiki A kan Kasar DRC

 

Babban mai shigar da kara na kotun kasa da kasa ta manyan laifuka, Karim Khan ne ya yi kira da a fito da wata sabuwar hanya ta fuskantar laifukan yakin da aka tafka a kasar DRC

Kotun kasa da kasar ta manyan laifukan wacce ta fara aiki tun a 2002, ta bude bincike a karon farko dangane da laifukan da aka tafka a gundumar Ituri dake yankin Arewa maso gabashin kasar DRC a 2004.

Da akwai kungiyoyi masu dauke da makamai da suka dauki shekaru 30 sun yin ta’annati akan albaraktun karkashin kasa a kasar DRC. Ya zuwa yanzu dai kotun ta yi shari’a akan laifuka uku da aka tafka a kasar ta DRC.

Khan ya fadawa manema labaru cewa; Mun yi shari’ar laifukan da aka aikata, sai dai har yanzu ana ba a daina yin fyade ba, laifuka ma ba a daina ba.

Babban mai shigar da karar na kotun kasa da kasar ya bayyana hakan ne dai bayan ganawarsa da Denis Mukwege, wanda ya taba samun kyautar Nobel ta zama lafiya saboda yadda ya rika taimakawa wadanda aka yi wa fyade.

Khan ya ce; Da akwai bukatar mu sauya salon yadda muke yin aiki tun a 2004, domin samo wata sabuwar hanya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya Za Ta Sauya Dabarar Aiki A kan Kasar DRC”