February 15, 2023

Kotun Koli ta dage sauraran kara kan canjin fasalin Naira zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu

Kotun koli a Najeriya a yau Laraba ta dage sauraran karar da gwamnonin Kaduna, Zamfara da Kogi suka shigar kan canja fasalin kudi.
Masu karar dai sun nemi Kotun da ta bada umarnin dakatar da canja fasalin Naira ga Babban Bankin Najeriya.
Sai dai biyo bayan zaman kotu da aka yi a yau Laraba, kotun ta dage sauraran karar zuwa ranar 22 ga watan Fabrairun wannan shekarar.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kotun Koli ta dage sauraran kara kan canjin fasalin Naira zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu”