Kotun Koli ta ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya wa fasali (N1000, N500, N200) har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.

Da take yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.
Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.
Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.
Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.
Tun da fari gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar da gwamnati ƙara, kuma ƙarar da suka shigar aka yi amfani da ita a matsayin hujja wajen yanke wannan hukunci.
A watan jiya kuma wasu gwamnoni suka ƙara bin bayansu wajen shigar da ƙarar, abin da ya janyo kotun ƙolin ta dakatar da wa’adin na wucin gadi da aka sanya na daina amfani da tsofaffin kuɗin.