March 24, 2023

Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da nasarar Adeleke a zaben jihar Osun

Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da nasarar Adeleke a zaben jihar Osun

Wata kotun daukaka kara wacce take zaune a birnin Abuja ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin Gwamnan jihar Osun.

Mai shari’a Mohammed Lawan Shuaibu ne ya jagoranci karar ya tabbatar da cewa dan takarar jam’iyar APC kuma tsohon gwamnan jihar ta Osun Goyega Oyetola ya gaza gabatar wa kotu da kwararan hujjoji kan tuhumar da yake na aringizon kuri’u da PDP ta yi a zaben gwamna da ya gabata a jihar ta Osun.

Kana kotun ta ci tarar jam’iyar APC da dan takararta kimanin naira N500,000.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kotun daukaka kara ta sake tabbatar da nasarar Adeleke a zaben jihar Osun”