October 21, 2021

Kotu ta yanke wa wasu daliban UNIMAID hukuncin shekaru 6 a gidan yari

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Wata babbar kotu dake garin Maiduguri ta jihar Borno ta yanke wa wasu mutane 18 ciki har da daliban jami’ar Maiduguri (UNIMAID) da makarantar “Ramat Poly” hukuncin shekaru 6 a gidan yari saboda laifin da aka same su da shi na kasancewa yan haramtacciyar kungiyar asiri.

Masu laifin dai an kama su ne a ranar 21 ga watan Satumbar 2019 a wani gidan saukar ba’ki dake garin Maiduguri lokacin da ake gudanar da bikin rantsar da sabbin mambobin da suka shiga kungiyar NBM.

Mai shari’a Umar Fadawu ya bayyana cewa hukuncin ya kasance ne bisa amsawar da suka yi cewa su ‘yan kungiyar asirin ne.

Alkalin kuma ya kara da cewa hukuncin da ya yanke musu din zata fara aiki daga ranar Laraba, 20 ga watan Oktobar wannan shekarar.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kotu ta yanke wa wasu daliban UNIMAID hukuncin shekaru 6 a gidan yari”