December 9, 2023

Kotu Ta Yanke Wa Sojan Da Ya Káshe Sheikh Goni Aisami Hukuncin Kisa

Kotu a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami hukuncin kisa ta hanyar rataya.

 

Kotun wadda ke zama a Potiskum ta yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan ta samu Lance Corporal John Gabriel da laifin kisan malamin.

 

Mai Shari’a Usman Zanna Mohammed ne ya sanar da hukuncin kisan kan Gabriel wanda a baya ke ƙarƙashin Bataliya ta 241 da ke Nguru.

 

Sannan kuma alkalin kotun ya yanke wa Lance Corporal Adamu Gideon hukuncin ɗaurin shekara goma a gidan yari sakamakon samunsa da laifin haɗin baki.

 

Kotun ta ce ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta yi dogon nazari kan irin hujjojin da aka gabatar a gabanta waɗanda suka gamsar da ita.

 

Sojojin da aka kama da laifin sun kashe fitaccen malamin ne bayan ya rage musu hanya da motarsa kan hanyar Kano zuwa Gashuwa a shekarar 2022.

 

Sheikh Goni Aisami fitaccen malami ne ɗan asalin garin Gashuwa a Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

 

Kafin rasuwarsa, Sheikh Goni Aisami fitaccen malamin Addinin Musulunci ne a Nijeriya daga garin Gashuwa na Jihar Yobe wanda yake gudanar da tafsirin Al-Kur’ani a fadar Sarkin Gashuwa da kuma sauran wurare.

 

Ahlulbaiti.com

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kotu Ta Yanke Wa Sojan Da Ya Káshe Sheikh Goni Aisami Hukuncin Kisa”