December 30, 2022

Kotu ta tabbatar da Oyebanji a matsayin gwamnan Ekiti

 

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan a Jihar Ekiti ta tabbatar da nasarar Biodun Oyebanji a zaben gwamnan da aka gudanar a watan Yunin 2022.

An bayyana Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG), a matsayin wanda ya yi nasara a zaben, bayan ya lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar.

Oyebanji na jam’iyyar APC, ya samu kuri’u dubu 187,057, inda ya doke Oni wanda ya samu kuri’u dubu 82,211, da Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u dubu 67,457.

 

©Daily Nigeria.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kotu ta tabbatar da Oyebanji a matsayin gwamnan Ekiti”