September 10, 2023

Komi Na Tafiya Daidai A Karamin Ofishin Jakadancinmu Na Paris

Iran ta bayyana cewa babu wani abun damuwa kawo yanzu game da aikin karamin ofishin jakadancinta a birnin Paris na faransa, bayan da wasu makiya tsarin juyin juya hali suka kai ofishin.

‘’Ba a katse ayyukan da ake yi a wurin ba kuma an kan shawo kan lamarin,” in ji mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na ofishin jakadancin Iran a birnin Paris a wata hira da ya yi da yammacin ranar Asabar, tare da IRNA.

A safiyar Asabar wasu mutane da ba a san ko su waye ba na kungiyoyin da ke fafutukar yakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasashen waje, sun kona tayoyi a kofar shiga karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris tare da haddasa hargisti.

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Komi Na Tafiya Daidai A Karamin Ofishin Jakadancinmu Na Paris”