September 19, 2021

Kogi: Yan Banga Sun Kashe Yan Bindiga 11 Tare Da Kama Jami’in NSCDC

Daga Balarabe Idriss


Wasu gamayyar yan banga sun yi nasarar hallaka yan bindiga 11 tare da damke wasu da yawa daga yan bindigan yayin wani farmaki da suka kai a wasu kauyuka dake yankin karamar hukumar Koto-Karfe jahar Kogi.
Baya ga wannan nasarar, a yayin farmakin sun damke wani jami’in “Civil Defence” wanda ake kira Abdullahi Saidu.

Farmakin ya wakana ne a tsakiyar daren juma’a yayin da yan bindigan suka kutsa cikin kauyen da nufin garkuwa da wasu zauna garin, sai dai kuma sun yi rashin sa’a inda bangaren yan banga dake yankin suka mayar musu da martanin ba-zata, a yayin da suka kwace mutum 3 daga cikin mutanen da yan bindigan suka dauka.

 

A bangare guda kuwa yan bangan sun yi nasarar damke wani jami’in “Civil Defence” tare da abokin sa, rahotanni sun bayyana cewa su biyun sun kasance suna safarar makamai da kuma kawo bayanan sirri ga yan bindigan.

 

Shugaban bangaren yada labarai na jahar Kogi, Mohammed Onogwu ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai yau a Legas, inda ya bayyana cewa mutum biyar daga yan bindigan hadi da jami’in “Civil Defence” din suna hannun jami’an fararen kaya na DSS don bincike.

Kana kuma ya kara da cewa irin wannan nasara abun murna ne babba da kuma hujja da ke nuna cewa harkar tsaro na da matukar tasiri da kuma karfi a jahar ta Kogi, ya kuma bayyana cewa kokarin da gwamnatin jahar ta Kogi take na ganin jahar ta kasance wacce ta fi kowacce jaha zaman lafiya a Najeriya yana tasiri.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kogi: Yan Banga Sun Kashe Yan Bindiga 11 Tare Da Kama Jami’in NSCDC”