June 22, 2023

Kogi: Mutane da dama sun rasa rayukan su a harin yan bindiga garin Ejule

 

Rahotanni da ke zuwa daga jihar Kogi na nuna cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Ejule dake karamar hukumar Ofu ta jihar.

Rahotannin dai sun ce harin ya fara ne da misalin karfe 3 na daren jiya inda aka yi asarar rayuwan wani dan Achaba da kuma matar wani mai sarautar gargajiya na garin. Inda dan Achaba ya samu ajalinsa sanadin wani harsashi da ya same shi kana ita kuma matar ta rasa rayuwarta a yayin da take kokarin neman mijin ta.

A bangare guda kuwa da akwai gidaje da suka kone a yayinda yan bindigan suka cinna musu wuta.

Mai bada shawara na musamman kan harkokin tsaro ga gwamnan jihar Kogi kwamanda Jerry Omadara ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kogi: Mutane da dama sun rasa rayukan su a harin yan bindiga garin Ejule”