June 28, 2022

Kissar wata kyakkyawar Budurwa, wacce kowa ke son ta

AMMA DAGA ƘARSHE WAYA SAME TA?

-Daga Emran Darussalam


An naqalto cewa: Wani matashi yace wa mahaifin sa: Ya mahaifi na, haƙiƙa naga wata yarinya kuma ina sonta da aure, kuma haƙiƙa ƙyan ta da ƙyan idanun ta sun burgeni.
Sai mahaifin cikin farin ciki yace: “Ya kai ɗa na a ina take domin in magantu da iyayen ta?

A yayin da suka je inda take tare kwatsam mahaifin wannan yaro yaga yarinya tayi mishi, sai yace wa yaron: Ya kai ɗa na ka saurare ni, a zahirin gsky wannan yarinya ba taka bace, sannan Baku dace da juna ba, wanda yafi da cewa da ita shine mutum iri na, wanda yake da gogewa a rayuwa, ta yanda zai iya kula da ita (idan ya aure ta).
Nan fa yaron yayi mamaki da jin kalaman mahaifin shi, sai yace wa mahaifin: gaskiya bazai yuwu ba, domim ni zan aure ta ba kai ba.

Haka sukai ta mujadala (a tsakanin su) har lamarin ya kai su ga ƴan sanda domin a warware musu matsalar, a yayin da kowanne yayi bayanin shi, sai wannan ɗan sanda yace musu:
Kuzo min da yarinyar domin mu tambayi wa take so a tsananin ku.
A yayin da aka zo da ita aiko sai ɗan sanda ya ganta yaji ta kwanta masa a zuciya, ya yaba da kyanta sosai, sai yace musu: wannan yarinya bata dace daku ba, tafi da cewa da mutum iri na.

Haka su ukun sukaita mujadala har lamarin ya kai su ga wazirin gari, domin ya sasanta tsananin su, a yayin da waziri ya ganta shima sai yace: Wannan ai ba mai auren ta sai waziri kama ta.
Haka sukaita Mujadala a tsakanin su, har lamarin ya kai su ga Sarki.

A yayin da suka iso fadan sarki sai yace: ni zan warware muku wannan matsala, kuzo min da ita, a yayin da aka zo da ita sai sarki ya ƙyalla ido ya ganta, sai yace: Wannan ai ba mai auren ta sai sarki kama ta, ni zan aure ta, haka suka samu saɓani sukaita mujadala a tsananin su.
Nan fa wannan budurwa tace musu: ni ina da mafita!

Yanzu zan fara gudu ku kuma ku bini a baya, duk wanda ya fara kama ni na yarda shi zai aure ni.

Haka kuwa lamarin ya kasance ta fara gudu, su biyar ɗin (saurayi, da mahaifin sa, da ɗan sanda da waziri da sarki suna binta da gudu).

Suna cikin gudun (suna binta a baya) kwatsam sai suka fada a rami mai zurfi dukkan su, sai wannan budurwa tazo dab da ramin, ta leqa su, sannan tace: yanzu kunsan koni waye? To nice DUNIYA!!!

Nice wacce dukkan mutane suke bina a guje, suna rige-rige wajen nema na, suna iya mantawa da addinin su (tare da ajiye shi a gefe sbd ni) har sai sun tsinci Kansu a ƙabari kuma basu same ni ba.

Kagaggen labari mai cike da wa’azi.

Ya Allah ka cire mana son duniya daga zukatan mu.

 

SHARE:
Rayuwar Iyali, Tarbiyyan Yara 0 Replies to “Kissar wata kyakkyawar Budurwa, wacce kowa ke son ta”