March 26, 2024

Kisan Ummita: Kotu ta yankewa Dan Chana da ya kashe budurwarsa hukuncin Kisa

 


Biyo bayan sauraron shaidu da kuma tara dukkan hujjoji, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji na wata babbar Kotu da ke zaune a Mila Road Bampai, ya tabbatar da zargin da ake yiwa Quandong Geng na kisan budurwarsa Ummita kuma bisa haka ya yanke masa hukuncin Kisa.

Al’amarin kisan dai ya faru ne a Watan Satumbar bara, inda Quandong ya kashe budurwarsa Ummukulsum Buhari ta hanyar soka mata wuka kana yayi kokarin guduwa.

A cewarsa, Marigayiyar ta yaudare shi ta hanyar karbar kudade a hannun sa kana kuma daga karshe ta Auri wani daban ba shi ba.

Duk kuwa da hujjojin da ya gabatar, daga karshe kotu ta yanke masa hukuncin kisa.

 

 

 

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Kisan Ummita: Kotu ta yankewa Dan Chana da ya kashe budurwarsa hukuncin Kisa”