November 23, 2023

Kisan Mata Da Kananan Yara Babbar Gazawa Ce Ga Isra’ila A Yakinta Kan Gaza

Shugaba Ibrahim Raeisi ya ce gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma dukkanin manufofinta ta hanyar kaddamar da yakin da take yi kan al’ummar zirin Gaza.

Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a birnin Tehran a yammacin jiya Laraba, tare da wakilan wasu gidajen talabijin na harshen Larabci guda biyar da suka hada da al-Manar ta kasar Labanon, al-Etejah ta Iraki, da gidan talabijin na al-Aqsa na Falasdinu da Falasdinu Al-yaum, da kuma tashar Masirah ta kasar Yemen.

Ya ce Isra’ila ba ta cimma ko daya daga cikin manufofinta na mamaye Gaza ba, da kuma yunkurin kawar da gwagwarmayar al’ummar Falastinu.

Har ila yau, yayin da yake ishara da yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi, Raeisi ya ce, “Abin da gwamnatin sahyoniyawan ta yi ya nuna gazawarta a fili, domin kuwa kisan mata da kanan yara da tsoffi da rusa masallatai da asibitoci da makarantu da sunan yaki da Hamas, wannan babbar gazawa ce ga Isra’ila.

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Kisan Mata Da Kananan Yara Babbar Gazawa Ce Ga Isra’ila A Yakinta Kan Gaza”